Mai Martaba Sarkin Daura, Alhaji Umar Faruq Umar, ya tabbatar wa Shugaban Kungiyar Kwadago Kasa (NLC) reshen Jihar Katsina, Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, da sarautar gargajiya ta Sarkin Gabas na Daura.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar manema labarai da fito daga Masarautar Daura, dauke da sa hannun Danejin Daura, Alhaji Abdulmuminu Salihu, a madadin Majalisar Masarautar.
Kwamared Hussaini Hamisu Yanduma, wanda shi ne Mataimakin Shugaban Kungiyar Ma’aikatan Lafiya ta Kasa, ya wannan sarauta ne saboda irin gudummuwar da yake bayarwa wajen ci gaban Masarautar Daura, da Jihar Katsina, da kuma Nijeriya baki daya.
Haka kuma, Sarkin Ban Daura Hakimin Yanduna ya tabbatarwa Kwamared Hamisu Hussaini Yanduma da sarautar gargajiya ta Sardaunan Yanduna.
A wata sanarwa mai dauke da sa hannun Sarkin Ban Daura, wanda kuma shi ne Hakimin Yanduna, Alhaji Mohammad Shazaalli, ya ce wannan karramawa ce saboda kyautatawa da ke tsakanin shi da al’ummar Yanduna.
A yayin da suke taya shi murna, Masarautar Daura da kuma Gundumar Yanduna sun yi kira a gare shi da ya ci gaba da kyawawan ayyukan da yake, tare da tabbatar da yakinin da al’umma suke da shi akan sa.