Jam’iyyun APC, PDP da NNPP a jihar Katsina sun gamu da babban koma baya a jihar bayan da dubban jiga-jigan ‘ya’yan jam’iyyun suka sauya sheka zuwa sabuwar hadaka ta ADC.
Daga cikin jiga-jigan PDP da suka koma ADC sun hada da tsohon sakataren gwamnatin jihar, Dr Mustapha Muhammad Inuwa da tsohon ministan tsaro a Nijeriya Lawal Batagarawa da tsohon sanata a shiyyar Daura Ahmed Babba Kaita da kuma Janar Maharazu Tsiga mai ritaya da sauran wasu jiga-jigai.
Da yake jawabi jim kadan bayan karbar katin zama dan jam’iyyar ADC, Dr Mustapha Muhammad Inuwa ya danganta wahalhalun da ‘yan Nijeriya ke fuskanta ga gwamnatin APC wajen gaza tabuka abin azo a gani ga fannoni daban-daban.
Tsohon sakataren ya ce sabon taken jam’iyyar ADC a Katsina “Nijeriya kowa yana ji a jikin shi, Katsina kuma akwai korafi in ji shi.